Shugaban na AU ya bayyana hakan ne a lokacin bude taron kungiyar tarayyar Afirka karo na 32 a jiya Lahadi a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, wanda ya samu halartar shugabannin kasashen Afrika, da jami'an diflomasiyya, da sauran muhimman mutane.
Da yake jawabi game da dangantakar dake tsakanin AU da Sin, Mahamat ya ce, bangarorin biyu suna kara samun muhimman sauye sauye daga dukkan fannoni.
Nasarar da aka samu a taron dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika (FOCAC) a Beijing a watan Satumbar 2018, ya kara bayyanawa a fili irin cigaban da ake samu game da batun dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu.
A watan Satumbar 2018, AU ta kaddamar da ofishin wakilcinta a Beijing, inda ya bayyana cewa, matakin zai kara karfafa danganatakar dake tsakanin bangarorin biyu. (Ahmad Fagam)