Emmanuel Nnadozie, babban sakataren gidauniyar bunkasa cigaban Afrika (ACBF), a ranar Litinin ya yabawa irin tallafin da kasar Sin ke bayarwa wajen bunkasa cigaban nahiyar Afrika.
Nnadozie ya bayyana hakan ne ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua, inda ya kara da cewa, "Mun jima muna sanya ido tare da nuna gamsuwa a fannonin daban daban na irin taimakon da gwamnatin kasar Sin ke bayarwa wajen bunaksa cigaban muhimman bangarorin da muke bukata,"
ACBF wata hukuma ce ta musamman mai fafutukar bunkasa cigaban kungiyar tarayyar Afrika AU.
Nnadozie ya kuma furta cewa, "Muna sane da irin dubban guraben karo ilmi da ake baiwa matasa 'yan kasashen Afrika domin yin karatu a kasar Sin kuma su koma gida Afrika bayan sun kammala domin taimakawa cigaban nahiyar."
Afrika ce babbar nahiyar da ta fi amfana daga tallafin raya cigaba na kasar Sin.(Ahmad Fagam)