A jiya Litinin wakilin kasar Sin ya bayyana cewa ya kamata a dauki matakai daban daban wajen inganta ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD.
Da yake jawabi a taron kwamitin musamman na wanzar da zaman lafiya, Wu Haitao, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, ya ce ayyukan wanzar da zaman lafiyar MDDr yana fuskantar sabbin kalubaloli duba da irin muhimmiyar rawar da yake takawa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaron kasa da kasa.
Wu kara da cewa, domin inganta tafiyar da ayyukan wanzar da zaman lafiyar, kamata ya yi sakatariyar MDDr ta kara kyautata dabarunta na samar da muhimman kayayyakin tafiyar da ayyukan, da kara horas da dakaru a lokacin da ake tura su bakin daga, da kuma yin amfani da wasu muhimman dabaru na tinkarar matsanancin hali da ake iya fuskanta. (Ahmad Fagam)