in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban jami'in kasar Sin zai gabatar da jawabi ga dandalin wanzar da zaman lafiya na kasa da kasa
2018-07-11 21:22:17 cri

Mamba a majalissar ba da shawara kan harkokin siyasa a kwamitin kolin JKS Yang Jiechi, zai gabatar da jawabi ga dandalin wanzar da zaman lafiya na kasa da kasa, wanda zai gudana nan gaba cikin wannan wata.

Da take tabbatar da hakan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Hua Chunying, ta ce Mr. Yang, wanda kuma shi ne darakta a ofishin lura da harkokin waje na kwamitin kolin JKS, zai gabatar da jawabin ne a jami'ar Tsinghua, a taron da zai wakana tsakanin ranekun 14 zuwa 15 ga watan nan na Yuli.

Jami'ar ta Tsinghua da hadin gwiwar cibiyar nazarin harkokin wajen kasar Sin ne za su dauki nauyin gudanar da wannan taro. Zai kuma hada manyan jami'ai daga sassa masu zaman kan su, domin tattauna batutuwa masu nasaba da tsaron kasa da kasa.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China