in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi gargadi game da sakankancewa da nasarar da aka samu kan kungiyar IS
2019-02-12 11:35:51 cri
Mataimakin Sakatare Janar na MDD mai kula da ofishin yaki da ta'addanci na majalisar, Vladimir Voronko, ya yi gargadi a jiya, game da sakankancewa da nasarar da aka samu kan kungiyar IS.

Vladir Voronko ya shaidawa kwamitin sulhu na majalisar cewa, duk da nasarar da aka samu a baya bayan nan kan kungiyar IS da abokan huldarta, har yanzu akwai yuwuwar samun barazana daga mayakan dake dawowa ko suke sake matsuguni, ko kuma daidaikun mutane da kungiyar ta yi tasiri kansu, wadda ya ce za ta iya bazuwa a duniya.

Ya ce duk da ayyukan mayakan IS na boye, har yanzu shugabancin kungiyar na da tasiri da kuma niyyar kai hare-hare sassan duniya, wanda zai taka muhimmiyar rawa wajen fadadar ayyukan kungiyar.

Ya kara da cewa, al'amarin zai iya kara muni la'akari da kalubalen da 'yan ta'adda baki wadanda ko suke barin yankunan da ake rikici ko suke komawa ko kuma wadanda ake gab da saki daga gidan yari za su haifar.

Don haka, Vladimir Voronko ya ce, wadanda ke kaura, da suka hada da wadanda suka kasa isa yankunan da ake rikici ko suka sauya hanya bisa umarnin kungiyar ko bisa radin kansu, ka iya ba da gudunmuwa wajen karuwar barazana, wanda tuni aka gani a nahiyar Turai da Kudu maso gabashin Asia. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China