in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban jami'in MDD ya taya murnar nasarar tattaunawar zaman lafiya tsakanin gwamnatin CAR da 'yan tawaye
2019-02-07 15:45:13 cri
Babban sakataren MDD Antonio Guterres a jiya Laraba ya bayyana sakon taya murnar cimma nasarar tattaunawar zaman lafiya tsakanin gwamnatin jamhuriyar tsakiyar Afrika CAR da kungiyoyin 'yan tawaye masu dauke da makamai a kasar, bayan da bangarorin biyu suka rattaba hannu kan yarjejeniyar.

"A wannan muhimmin biki na sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta kasa da kasa tsakanin gwamnatin jamhuriyar tsakiyar Afrika da kungiyoyi masu dauke da makamai, a ranar 6 ga watan Fabrairu a Bangui, babban sakatare yana taya dukkan masu ruwa da tsaki da suka jagoranci samun nasarar kammala tattaunawar zaman lafiyar wanda ya gudana a Khartoum, na kasar Sudan," kakakin mista Guterres shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa.

Babban jami'in MDD ya yabawa rawar da shugabancin kungiyar tarayyar Afrika AU ta taka wajen shirya tattaunawar, wanda aka gudanar tare da goyon bayan MDD, sanarwar ta kara da cewa, Guterres ya bukaci masu ruwa da tsaki da su kara tsayawa tsayin daka domin ganin an kammala aiwatar da dukkan yarjejeniyar cikin wa'adin da aka diba. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China