in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabar zaman MDD ta gabatar da sakon taya murnar shiga sabuwar shekarar Sinawa
2019-02-06 15:59:07 cri
Shugabar zaman MDD karo na 73 Maria Fernanda Espinosa, ta gabatar da sakon taya murnar shiga sabuwar shekarar Sinawa, ga daukacin al'ummar kasar Sin.

"A wannan lokaci da ake ci gaba da bukukuwan sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta al'ummar Sinawa, ina mika sakon gaisuwa ta musamman ga Sinawa. Ina musu fatan koshin lafiya, zaman lafiya da jin dadi! Barka da sabuwar shekara!" a wani sakon tweeter da Uwar gida Espinosa ta fitar da yaren Sinanci.

A ranar Litinin ne dai BMMMD Antonio Guterres, ya gabatar da sakon sa na taya murnar shiga sabuwar shekara ta Sinawa, bisa kalandar gargajiyar kasar. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China