Ma Zhaoxu wanda shi ne wakilin musammam na Shugaban kasar Sin Xi Jinping a wajen taron Kwamitin Sulhu na MDD kan ayyukan sojojin haya a Afrika, ya ce ayyukan sojojin haya na barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin kasashen Afrika, kuma kasar Sin na kira da kasashen duniya su kara kokarin magance matsalar.
Ya ce wadanan ayyukan na katsalandan ga harkokin cikin gidan kasashe masu tasowa da take cikakken iko da 'yancinsu, ya na mai cewa kasar Sin ba ta goyon bayan ayyukan ko kadan.
Wakilin na kasar Sin, ya kuma bukaci al'ummomin kasashen waje su taimakawa kasashen Afrika wajen gaggauta samun ci gaba da rage fatara da kawar da tushen matsalolin dake haifar da rikici da kuma inganta ci gaban tattalin arziki da zaman takewar kasashen nahiyar.
Ma Zhaoxu, ya kuma yi alkawarin Sin za ta ci gaba da marawa nahiyar Afrika baya, wajen samun zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaba, inda ya bayyana fatan Sin da Afrika za su hada hannu wajen gina al'umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya. (Fa'iza Mustapha)