Ma Zhaoxu, ya yi wannan kira ne, yayin taron kwamitin tsaron MDD na jiya Talata, yana mai cewa Sin na iya kokarin ta, na taimakawa kasashen wannan yanki, wajen tsara manufofi, da hada sassan dabaru da ayyuka, domin karya lagon manyan laifuka da ake aikatawa a teku, matakin da zai kai ga samar da ci gaba, da wadata a kasashen shiyyar.
Kaza lika jami'in ya ce a shekarun baya bayan nan, duk da cewa an samu raguwar ayyukan 'yan fashin teku a zirin Aden, a hannu guda ana fuskantar matsalar tsaro a zirin Guinea dake yankin yammacin Afirka, wanda hakan ya yi matukar tasiri ga ci gaban tattalin arziki da zamantakewar kasashe masu makwaftaka da gabar tekun. (Saminu Hassan)