Sakatare janar na MDD Antonio Guterres ya ce nahiyar Afrika ta zamanto abin misali game da warware tashe tashen hankula cikin lumana a fadin nahiyar.
Jami'in MDDr ya yi wannan tsokaci ne a taron manema labarai a gefen taron kungiyar tarayyar Afrika AU karo na 32.
"Na yi amana Afrika ta kasance abin misali wajen warware matsaloli da rikice rikice,"inji Guterres. "Na tabbata wannan kwarin gwiwa da ta nuna zai cigaba da yaduwa zuwa sassan duniya."
Guterres ya kara bayyana muhimmancin hadin gwiwar dake tsakanin MDD da AU wajen daukar matakan riga kafin barkewar tashin hankali da warware dukkan tashe tashen hankula a kasashen Afrika.
Kana ya yabawa kasashen Afrika musamman wajen daukar nauyin 'yan gudun hijira daga wasu daga cikin kasashen nahiyar duk kuwa da karancin kudaden tafiyar da ayyuka da ake fama da su.(Ahmad Fagam)