A wajen taron shugabannin kasashen Afirka mai taken "zuba jari ga lafiyar jama'a" da aka yi a Addis Ababa, fadar mulkin kasar Habasha, Paul Kagame ya yi jawabin cewa, ya zama tilas kasashen nahiyar su karfafa hadin-gwiwa a karkashin ajandar bunkasa Afirka nan da shekara ta 2063, da kara fadada kashe kudade a bangaren kiwon lafiya, gami da karfafa gwiwar kamfanoni masu zaman kansu don su zuba jarinsu a wannan fanni.
Shi ma a nasa bangaren, Moussa Faki Mahamat, shugaban kwamitin AU ya ce, ya kamata a kara zuba jari a fannin kiwon lafiya na Afirka, duba da raunin muhimman ababen more rayuwar jama'a ta fannin kiwon lafiya gami da tabarbarewar matsalar kiwon lafiya a wannan nahiya.
Bisa alkaluman da AU ta fitar, an ce, duk da cewa kasashen Afirka sun kara zuba kudade a bangaren kiwon lafiya, amma akwai kasashe biyu kawai a cikin membobin AU wadanda ke amfani da kashi 15 bisa dari na kasafin kudin kasar ko fiye da haka wajen goyon-bayan harkokin kiwon lafiya. Har wa yau, a halin yanzu, kimanin rabin mutanen Afirka ba su iya samun kayan kiwon lafiya da suke bukata ba, har ma a ko wace shekara akwai miliyoyin mutane wadanda suke mutuwa a sakamakon wasu cututtuka masu yaduwa na yau da kullum.(Murtala Zhang)