in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Aiwatar da yarjejeniyar ciniki ta AfCFTA zai kara kashi 15 bisa 100 na cinikayyar nahiyar Afrika
2019-02-10 15:42:00 cri

Jami'in bankin raya cigaban Afrika (AfDB) ya ce, aiwatar da yarjejeniyar ciniki maras shinge a tsakanin kasashen nahiyar Afrika (AfCFTA), ana sa ran zai kara karfafa cinikayya a tsakanin nahiyar da kashi 15 bisa 100.

Hanan Morsy, daraktan sashen kula da raya kananan sana'o'i na bankin AfDB ya ce, aiwatar da yarjejeniyar ta AfCFTA zai samar da kudaden shigar kasashen Afrika wanda ya kai dala biliyan 2.8, kamar yadda ya bayyana ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua a Addis Ababan kasar Habasha.

Kasashen Afrika za su aiwatar da yarjejeniyar ce ta hanyar samar da wasu dokoki na cikin gida wadanda za su kawar da kudaden haraji a harkokin cinikayya tsakanin kasashen, da kawar da shinge a sha'anin cinikayya da ayyukan hidima, da bude hanyoyin sama na zirga-zirgar sufurin jiragen sama a kasashen na Afrika domin bada damar shigi da ficin kayayyaki a tsakanin iyakokin kasashen nahiyar.

A ranar Alhamis, ana sa ran wasu karin kasashen mambobi AU su 6 za su gabatar da amincewarsu ga yarjejeniyar ta AfCFTA, inda adadin da suka amince da yarjejeniayr zai karu zuwa 17.

Kungiyar tarayyar Afrika ta ce ana bukatar kasashe 22 su amince da yarjejeniyar ta AfCFTA kafin ta fara aiki gadan-gadan, matakin da zai taimaka wajen kafa wata yarjejeniyar ciniki cikin 'yanci mafi girma a duniya a 'yan shekaru baya bayan nan.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China