in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tsohon Firaministan Habasha zai jagoranci tawagar masu sanya ido a zaben Nijeriya
2019-02-09 16:00:54 cri
Tsohon Firaministan Habasha, Hailemariam Desalegn, zai jagoranci tawagar Tarayyar Afrika dake sa ido kan harkokin zabe domin sa ido a babban zaben Nijeriya dake karatowa.

Da take jawabi yayin wani taron manema labarai a hedkwatar Tarayyar dake birnin Addis Ababa na Habasha, kwamishinar AU mai kula da harkokin siyasa Minata Samate Cessouma, ta ce Hailemariam Desalegn zai jagoranci tawagar tarayyar masu sa'ido kan zabe a babban zaben Nijeriya, kasa mafi yawan al'umma a nahiyar Afrika.

A cewar Minata Cessouma, Nijeriya kasa ce mai muhimmanci a fadin Afrika, a fannin al'umma da tattalin arziki. A don haka ba sa bukatar wani tashin hankali da zaben zai haifar. Ta kara da cewa, dukkan abokan hulda ciki har da AU, za su yi aiki tare wajen tabbatar da sahihin zabe mai adalci ya gudana a kasar.

Nijeriya za ta gudanar da babban zabenta ne a ranar 16 ga watan nan, inda za a fara da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya, sannan a gudanar da na gwamnonin da na 'yan majalisun dokokin jihohi a ranar 2 ga watan Maris na bana. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China