in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta bukaci kasashen Afrika su inganta kokarin tabbatar da yarjejeniyar ciniki cikin 'yanci
2019-02-08 16:13:45 cri
Shugaban hukumar Tarayyar Afrika AU, Moussa Faki Mahamat, ya bukaci kasashe mambobin kungiyar, su matse kaimi wajen tabbatar da yarjejeniyar kafa yankin ciniki cikin 'yanci na nahiyar Afrika.

Moussa Faki Mahamat ya yi kiran ne yayin zama na 34 na majalisar zartaswar kungiyar, wanda ke gudana daga 7 zuwa 8 ga wata, a hedkwatar AU dake birnin Addis Ababa, wanda ke gudana karkashin tsare-tsaren zaman babban zauren kungiyar na 32.

Shugaban ya ce nasarar da aka samu game da yarjejeniyar abun karfafa gwiwa ne, yana mai cewa la'akari da yadda ake amincewar kunshin yarjejeniyar, za su iya sa ran shiga yarjejeniyar ka'in da na'in cikin makonni masu zuwa

Har ila yau, ya ce yana fatan kasashe 6 da suka rage ba su amincewar kunshin yarjejeniyar ba, za su sanya hannu nan ba da jimawa ba, kana wadandan suka riga suka sanya hannu kuma, za su gaggauta aiwatar da shi. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China