Harin wanda ya abku a ranar Lahadin da ta gabata, a garin Aguelhok dake yankin Kidal na kasar Mali, ya kuma jikkata a kalla wasu 25.
Bayan da sakon ta'aziya da ya aikewa gwamnatin Chadi da iyalan wadanda suka rasa rayuka, shugaban hukumar gudanarwar ta AU ya bukaci hukumomin kasar Mali da kungiyoyin 'yan tawaye da suka sa hannu kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta na kasar, da su yi kokarin zakulo wadanda suka aikata wannan mummunan aiki don su girbi abin da suka shuka.
Faki ya bayyana fatansa na ganin wadanda suka ji rauni sun samu sauki cikin sauri, Ya kuma gode musu a madadin daukacin jama'ar nahiyar Afirka a bisa jaruntan da suka nuna. (Bello Wang)