in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sudan ta kudu ya zargi kasashen yamma da kawo cikas game da zaman lafiyar kasar
2019-02-08 20:25:23 cri
Shugaban kasar Sudan ta kudu Salva Kiir a yau Juma'a ya zargi masu bada taimako na kasashen yammacin duniya da gazawa wajen kin samar da kudaden da za'a yi amfani da su wajen aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya wanda zai kawo karshen yakin basasar kasar da aka shafe sama da shekaru biyar ana fuskanta a kasar.

Kiir wanda ya bayyana hakan ga wasu manyan jami'an jam'iyya mai mulki ta Sudan People's Liberation Movement (SPLM), inda ya ce, kasashen yamma da al'ummomin kasa da kasa masu samar da agajin kudade sun dauki wata irin al'ada ta "bari mu zuba ido mu gani" a matsayin wata hanyar dake kawo tsaiko wajen aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiyar kasar wacce aka cimma matsaya kanta a watan Satumbar bara. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China