in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta yi Allah wadai da cin zarafin mata da 'yan mata a Sudan ta kudu
2018-12-13 11:00:35 cri
A jiya Laraba kungiyar tarayyar Afrika AU, ta fitar da wata sanarwa inda ta yi Allah wadai da cin zarafin mata da 'yan mata ta hanyar lalata da su a Sudan ta kudu.

A wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, wakiliyar musamman mai kula da tsaro da zaman lafiyar mata ta kungiyar AU, Mme Bineta Diop, ta sanar da cewa, rahotannin baya bayan nan sun nuna cewa kimanin mata da 'yan mata 150 ne aka yi wa fyade da kuma dukansu a garin Bentiu dake Sudan ta kudu.

Diop, ta bukaci masu ruwa da tsaki a matakan shiyya, nahiya da matakan kasa da kasa da su kai daukin gaggawa domin ceto matan da aka ci zarafinsu ta hanyar lalata a Sudan ta kudun.

Tun bayan barkewar yakin basasa a watan Disambar shekarar 2013 a Sudan ta kudu, wanda aka samu ruruta wutar rikicin sakamakon banbancin kabila da nuna son zuciya, an yi kiyasin dubban mutane ne rikicin ya yi sanadiyyar salwantar rayukansu, kana wasu mutanen kusan miliyan 4 tashin hankalin ya raba su da matsugunansu. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China