Hukumar hadin gwiwa mai sanya ido da bin diddigi (RJMEC) ta bukaci a gudanar da cikakken bincike game da harin da aka kaddamar kan tawagar jami'an dake sanya ido kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta dake kasar (CTSAMVM).
"Muna sa ran gwamnati za ta gudanar da cikakken bincike na adalci ba tare da bata lokaci ba, kuma wadanda aka samu da hannu a gurfanar da su gaban shari'a," masu sanya idon ne suka bayyana cikin wata sanarwar da aka fitar a Juba.
Masu sanya idon sun bukaci gwamnati da ta dauki matakan da suka dace wajen hana sake afkuwar hakan a nan gaba, a yayin da shirin wanzar da zaman lafiyar kasar Sudan ta kudu ke ci gaba da gudana. (Ahmad Fagam)