in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An hallaka mutane 42 yayin wani tashin hankali a Sudan ta kudu
2019-01-09 20:43:31 cri
A kalla mutane 42 sun rasa rayukan su, kana wasu 78 sun jikkata yayin wani tashin hankali, wanda ya biyo bayan wani hari da wasu 'yan bindiga suka kai kan wasu makiyaya a jihar Bieh ta Sudan ta kudu.

Gwamnan jihar Akobo Johnson Gony Bilu, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, tashin hankali ya barke ne tun daga ranar 6 ga watan nan na Janairu, sa'an nan ya fantsama zuwa yankunan Akobo, da Nyirol ta gabas dake kudancin kasar Sudan ta kudu. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China