Babban kwamishina a hukumar dake lura da 'yan gudun hijira ta MDD ko UNHCR a kasar Uganda Joel Boutroue, ya ja hankalin shugabannin Afirka, da su maida hankali ga dalilan dake sabbaba gudun hijira a sassan nahiyar.
Joel Boutroue, ya yi wannan kira ne yayin taron jagororin Afirka da ya gudana a birnin Addis Ababa fadar mulkin kasar Habasha a karshen makon jiya. Kiran na Mr. Boutroue, na zuwa ne yayin da jagororin nahiyar suka gudanar da taron bankado sahihan hanyoyin magance kalubalen 'yan gudun hijira dake addabar nahiyar.
A jiya Laraba, Mr. Boutroue, ya shaidawa manema labarai cewa, kungiyar hadin kan kasashen Afirka ta AU, ta sanya shekarar bana a matsayin shekarar 'yan gudun hijira, da masu dawowa daga gudun hijira, da wadanda ke samun mafaka a wasu yankuna na kasashen su, wanda hakan ya shaida irin muhimmancin da nahiyar ke dorawa kan batun 'yan gudun hijira.
Jami'in ya ce yana fatan kungiyar ta AU, za ta maida hankali ga manyan dalilan dake haifar da kaurar jama'a a dukkanin sassan nahiyar baki daya. (Saminu Hassan)