Cikin wani rahoto da ta wallafa a baya-bayan nan mai taken 'har yanzu babu mafita ga matsalar 'yan gudun hijira a Afrika" , cibiyar ISS wadda ke zaman kanta a Afrika, ta jadadda muhimmancin da ke akwai na samar da mafita mai dorewa game da matsalar 'yan gudun hijira a nahiyar, a matsayin hakki na bai daya da ya rataya a wuyan dukkan kasashe.
Rahoton, wanda ya bayyana kasashen nahiyar 3 da suka hada da Burundi da Nigeria da Sudan ta Kudu a matsayin na 6 cikin jerin wuraren da hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD UNHCR ke ba muhimmanci, ya kuma bayyana cewa, rashin kwanciyar hankali da take hakkokin bil adama da rikice-rikicen dake aukuwa a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya da Jamhuriyar Demokradiyyar Congo da Eritrea da Mali da Somalia da Sudan, sun kara tsananta, haka zalika yanayin 'yan gudun hijira a kasashen da yankunansu.
Rahoton ya kuma nuna cewa, matsalar 'yan gudun hijira za ta fadada daga yankin tafkin Chadi ta ratsa yankin manyan tabkuna zuwa kahon Afrika, inda a yanzu haka yankin kudu da hamadar sahara ke dauke da kimanin 'yan gudun hijira miliyan 6.3, kwatankwacin 1/3n jimilar 'yan gudun hijira na duniya.
Rahoton 2017 da hukumar UNHCR ta fitar ranar Talata da ta gabata, ya nuna cewa, kasashe masu tasowa ne ke ba kaso 85 na 'yan gudun hijirar mafaka, kuma cikin kasashen, har da na Afrika. (Fa'iza Mustapha)