in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNHCR ta kwashe 'yan gudun hijira 133 daga Libya zuwa Niger
2018-12-07 10:59:07 cri

Hukumar kula da 'yan gudun hijira da MDD (UNHCR) a jiya Alhamis ta kwashe 'yan gudun hijira 133, da suka hada da mata da kananan yara daga kasar Libya zuwa Jamhuriyar Niger.

"hukumar kula da 'yan gudun hijirar tare da hadin gwiwar hukumomin kasar Libyan, sun kwashe 'yan gudun hijirar 133 daga Libya zuwa Niger bayan karbar bakuncinsu a wani waje da aka tanada don tsugunar da su (GDF), wanda aka bude a Tripoli a ranar Talata," inji shirin wanzar da zaman lafiya na MDD a Libya.

Sabon wajen na GDF, ma'aikatar kula da harkokin cikin gidan Libya ce ke tafiyar da wajen, tare da tallafin UNHCR, da hukumar bada agaji ta LibAid, da nufin samar da muhalli mai inganci ga marasa galihu wajen samar musu da mafita, ciki har da batun sake tsugunar da 'yan gudun hijirar, da sake sada su da iyalansu, da kwashe su don mayar da su kasashensu, da dai sauransu, inji sanarwar.

"A cibiyar, UNHCR da abokan hulda suna samar da kayayyakin jin kan al'umma kamar wararen zama, abinci da magunguna da kuma tallafawa wajen seta tunani. Da janyo kananan yara jiki da bada kariya ga jami'ai domin tabbatar da kiyaye 'yan gudun hijirar da masu neman mafaka yadda ya kamata," inji sanarwar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China