Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta kasar Norway mai ayyukan jin kai, ta ce tun daga watan Janairun bana, rikice-rikice ko iftila'i sun raba mutane miliyan 2.7 da matsugunansu a nahiyar Afrika.
Sabon rahoton na cibiyar dake bibiyar harkokin 'yan gudun hijira ta hukumar kula da 'yan gudun hijirar ta Norway, wanda ya ce mutanen ba su ketara kasashen waje ba, ya ce a kowacce rana, mutane 15,000 ne ke rasa matsugunansu a nahiyar.
Rahoton ya ce, galibin 'yan gudun hijirar sun kasance a kasashe da ba su da karfin fuskantar matsalar, da kuma rashin kwakkwaran shugabanci, inda ya ce, suna rayuwa ne cikin matsanancin hali.
A cewar hukumar, wannan shi ne halin da galibin 'yan gudun hijirar Afrika miliyan 12.6 su ke ciki a karshen shekarar 2016.
Har ila yau, rahoton ya ce rikici ya haddasa kashi 75 bisa dari na 'yan gudun hijira a rabin farkon shekarar nan, da kaso 70 cikin shekarar 2016.
Jamhuriyar Demokradiyyar Congo da Sudan ta kudu da Nijeriya na daga cikin kasashe 5 da matsalar ta fi kamari.
Ya kuma yi kira ga hukumomin raya kasashe su hada hannu da masu aikin jin kai wajen karewa da rage 'yan gudun hijira a cikin kasashen, tare da samar da dawwamamiyar mafita ga miliyoyin mutane da matsalar ta shafa. (Fa'iza Mustapha)