Da yake tabbatar da hakan yayin wani taron manema labarai a jiya Talata, mai magana da yawun hukumar lura da 'yan gudun hijira ta MDD UNHCR Mr. Babar Baloch, ya ce hukumar sa da sauran abokan huldar ta na aiki tukuru, don ganin sun ba da agajin jin kai ga 'yan gudun hijirar. Tuni kuma suka yiwa irin wadannan masu neman mafaka su kimanin 2,000 rajista.
Baloch ya kara da cewa yanzu haka ma akwai wasu karin masu gudun hijirar su 3,000 da ba a riga an yi masu rajista ba. Baya ga wasu da dama da ake zaton na makale a sassan wasu dazuzzuka, a kokarin su na tsallakawa zuwa Najeriyar.
UNHCR dai ta ce tana aiki da mahukuntan Najeriya, da ma wasu hukumomin MDD wajen tsara bukatun 'yan gudun hijirar, tare da tunkarar aikin agazawa masu neman mafakar, wadanda nan gaba ka iya kaiwa 40,000. (Saminu)