in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani kamfanin zirga-zirgar sararin samaniya na kasuwanci na kasar Sin yana shirin kera taurarin dan-Adam bisa fasahar AI
2018-11-26 09:28:08 cri
Kamfanin zirga-zirgar sararin samanin kasuwanci na kasar Sin mai suna Chengdu GuoXing Aeorospace Techonolgy Ltd yana shirin kaddamar da wani tauraron dan-Adam a watan Disamba mai kamawa, bayan nasarar harba wasu taurarin dan-Adam guda biyu cikin kwanaki 100 bayan kafa shi.

Shi dai wannan kamfanin wanda ke samun tallafin karamar hukumar yankin, an kafa shi ne a lardin Sichuan dake kudu maso yammacin kasar Sin. Ya kuma yi nasarar kera wasu taurarin dan-Adam na gwaji ta hanyar amfani da fasahar kere-kere ta AI.

Rahotanni na cewa, yanzu haka kamfanin ya dauki sama da ma'aikata 40, galibinsu 'yan kasa da shekaru 30 da haihuwa, wannan misali daya ne daga masana'antar zirga-zirgar sararin samaniyan kasar Sin na kasuwanci dake bunkasa.

Wani rahoto da cibiyar dake bibiyar harkokin zuba jari a bangaren zirga-zirgar sararin samaniya da ake fatan rayawa a nan gaba dake da mazauni a nan birnin Beijing, ya nuna cewa, a cikin shekaru uku da suka gabata sama da kamfanonin kasar Sin masu zaman kansu guda 60 sun shiga harkar zirga-zirgar sararin samaniya na kasuwanci, in da suka mayar da hankali wajen kerawa da kuma harba taurarin dan-Adam da kuma rokoki.

An yi kiyasin cewa, darajar kasuwar zirga-zirgar sararin samaniya ta duniya za ta kai dala biliyan 485 a shekarar 2020, inda aka yi kiyasin darajar kasuwanci a bangaren kasar Sin za ta kai Yuan biliyan 800, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 125.78. Ana kuma ganin cewa, nan da shekaru goma masu zuwa, kaso biyu cikin uku na masu bukatar taurarin dan-Adam a duniya za su fito ne daga bangaren 'yan kasuwa. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China