in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhu na MDD zai gudanar da muhawara kan kawar da makamai a Afrika
2019-02-02 15:45:58 cri
Kwamitin sulhu na MDD, zai gudanar da wata budaddiyar muhawara, kan shirin Tarayyar Afrika na "kawar da makamai a Afrika", a cikin watan nan na Faburairu.

Shugaban kwamitin Anatolio Ndong Mba na watan Faburairu, wanda kuma shi ne jakadan kasar Equatorial Guinea a MDD, ya shaidawa wani taron manema labarai cewa, kwamitin zai kuma shirya muhawarar manyan jami'ai game da ayyukan sojojin haya, a matsayin abun da ke haifar da rashin tsaro da zaman lafiya a Afrika, inda za a mayar da hankali kan yankin tsakiyar nahiyar.

Haka zalika, ya ce za a kuma shirya wata muhawarar kan laifuffukan da ake aikatawa kan iyakokin kasa da kasa a cikin teku.

Jakadan ya ce har yanzu, ana tattaunawa kan aikin na wannan watan, domin akwai matakin da za a kai da sai an cimma yarjejeniya a kai.

Kamar yadda aka shirya, kwamitin zai kai ziyarar aiki kasashen Cote d'Ivoire da Guinea Bissau a cikin wannan wata, inda shugaban kwamiti na wannan wata ya ce manufar ziyarar ita ce, karfafawa shugabannin siyasar Guinea-Bissau gwiwar tabbatar da sahihin zabe cikin lumana, da za a dama da kowa da kowa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China