Stephane Dujjaric ya ce ya kamata a kara agajin sosai ta yadda zai dace da mutane dake kara kwarara, inda wasu kuma suke kin komawa garin Rann ko sansaninsu dake Ngala, ba tare da samun tabbacin tsaro ba.
Yayin taron manema labarai da aka saba yi, Stephane Dujjaric ya shaidawa manema labarai cewa, ma'aikatan agaji na aiki tare da hukumomi, wajen kare hakkin 'yan gudun hijirar na samun mafaka tare da sauya musu matsuguni zuwa yankunan dake da tsaro, wadanda ke nesa da bakin iyakar kasar.
Kimanin 'yan gudun hijirar Nijeriya 35,000 ne suka tsere zuwa Kamaru. (Fa'iza Mustapha)