in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hare-hare sun yi sanadin mutuwar jami'an wanzar da zaman lafiya na MDD guda 26 a shekarar 2018
2019-02-01 11:14:36 cri

Jami'an wanzar da zaman lafiya da wasu jami'ai masu alaka da su na MDD 26, da fareren hula 8 ne suka mutu a bakin aiki, sanadiyyar hare-hare a shekarar 2018.

Kakakin Sakatare Janar na MDD Stephane Dujarric ya bayyana a jiya yayin taron manema labarai da aka saba yi cewa, yawan wadanda suka mutu a shekarar 2018 shi ne adadi mafi kasa da aka samu a cikin shekaru 5 da suka gabata, kuma bai kai rabin adadin wanda aka samu a 2017 ba.

Da yake bayyana rahoton kungiyar ma'aikatan MDD, kakakin ya ce, shirin wanzar da zaman lafiya a Mali ne ya fi asarar rayuwa, inda aka kashe jami'ai 11. Shirin wanzar da zaman lafiya a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ne ke bi masa, inda aka kashe jami'ai 8. Sai kuma Jamhuriyar Afrika ta tsakiya da aka kashe mutum 7.

Shugabar kungiyar ma'aikata Bibi Sherifa Khan, wadda ta ce ma'aikatan MDD na aiki a wurare mafi hadari a duniya, ta ce duk wani yunkuri na rage kasafin kudin aiwatar da ayyukan wanzar da zaman lafiya na kara jefa ma'aikatan cikin hadari, tare da yin barazana ga manufofi da burikan hukumar. (Fa'iza Msutapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China