Wannan mataki ya sa tekun ya zama mafi hadari, wajen masu yunkurin tsallaka shi, duk kuwa da raguwar bakin haure da ke bin wannan hanya domin isa sassan nahiyar ta Turai.
UNHCR ta fitar da wani rahoto a Larabar nan, mai taken "Tafiyar masu Naci", wanda a cikinsa ta ce adadin masu yunkurin tsallakawa Turai ta tekun ya kazanta a shekarar bara, ko da yake an rika gudanar da ayyukan dakilewa, da na ceton wadanda suka nutse a tekun.
Rahoton ya ce bisa jimilla, bakin haure da 'yan gudun hijira 139,300 ne suka isa Turai a shekarar ta 2018, adadin da shi ne mafi karanci cikin shekaru 5 da suka gabata. (Saminu Hassan)