"Kasar Sin a ko da yaushe tana adawa da yin katsalandan kan al'amurran da suka shafi cikin gidan wata kasa, kana tana Allah wadai da shisshigin da wasu kasahen duniya ke yi a harkokin cikin gidan kasar Venezuela," in ji Ma Zhaoxu, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD.
Ba komai ba ne "halin da ake ciki a Venezuela ya shafi harkokin cikin gidanta ne," Ma ya ce, wannan batu "bai kasance barazana ga zaman lafiya da tsaron kasa da kasa ba, kuma ba wata ajanda ba ce da ta shafi kwamitin sulhun MDD."
"Kasar Sin tana adawa da sanya batun kasar Venezuela cikin ajandar kwamitin sulhun MDD," jakadan ya kara da cewa, harkokin kasar Venezuela al'ummar kasar ne kadai suke da ikon warware matsalarsu da kansu.
"Muna kira ga dukkan bangarorin da abin ya shafa da su mutunta zabin da al'ummar kasar Venezuelan suka yi wa kansu", in ji jakadan na kasar Sin. (Ahmad Fagam)