Babban jami'in MDD ya aike da sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda hadarin ya rutsa da su, in ji Farhan Haq, mataimakin kakakin babban sakataren MDD.
"MDD a shirye take ta tallafawa hukumomin da abin ya shafa a kasar Brazil a kokarin da suke na aikin bada ceto da samar da kayan tallafi, in ji Haq.
A kalla mutane 34 ne aka bada rahoton mutuwarsu bayan madatsar ruwan mallakin kamfanin hakar ma'adanai Vale ya balle da yammacin ranar Juma'a a jahar Minas Gerais dake kudu maso gabashin kasar ta Brazil. Ballewar dam din ta haifar da gagarumar barna ga gidajen kwanan jama'a da yankin baki daya. (Ahmad Fagam)