in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Amurka sun kara zafafa kai hare-hare ta sama a Somalia
2019-01-25 10:11:04 cri
Rundunar sojojin kasar Amurka ta bayyana cewa, dakarunta sun kara zafafa kai hare-hare ta sama a kasar Somaliya, da nufin kawar da kungiyar mayakan al-Shabab a kasar dake kahon Afirka.

Dakarun Amurka da Afirka (Africom) sun bayyana cewa, a ranar Laraba ma, sun kai hari sau biyu kan sansanin mayakan na Al-Shabab a kusa da Jilib da yankin tsakiyar Juba, amma ba su yi wani karin haske game da adadin wadanda suka jikkata ba.

A cewar Africom, ta karfafa hare-hare ta sama kan kungiyar 'yan ta'adda a kasar ta Somaliya ne, amma babu wani farar hula da aka kashe ko ya jikka sanadiyar hare-hare da suka kaddamar.

A ranar 19 ga watan Janairu ma, dakarun Amurka dake kasar, sun kaddamar da hari ta sama kan wadannan yankuna, inda suka kashe mayakan al-Shabab 52. Hari ta saman dai martani ne kan wani hari ta sama da kungiyar ta kaddamar kan sojojin kasar ta Somaliya.

A 'yan watannin nan sojojin Amurka sun yi amfani da jirage marasa matuka, wajen kaddamar da jerin hare-hare ta sama kan mayakan na al-Shabab da na IS, yayin da tawagar kungiyar AU dake aikin wanzar da zaman lafiya ke shirin janyewa daga kasar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China