in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Amurka sun kashe mayakan al-Shabab 52
2019-01-20 15:50:43 cri
Babban ofishin kasar Amurka dake nahiyar Afirka wato AFRICOM a takaice ya bayar da sanarwa a daren jiya cewa, sojojin saman Amurka sun yi luguden wuta kan wata matattarar kungiyar al-Shabab a kusa da garin Jilib dake kudancin kasar Somaliya, al'amarin da ya yi ajalin dakarun kungiyar su 52.

A cewar sanarwar, harin dai ya kasance martani ne da sojojin Amurkan suka mayar kan farmakin da dakarun al-Shabab din suka kai kan sojojin gwamnatin Somaliya a kwanakin baya, inda ba'a samu jikkatar fararen hula ba.

Rahotanni daga kamfanin dillancin labaran Somaliya sun ce, da safiyar jiya Asabar, wasu mayakan al-Shabab sun kai hari kan wani barikin soja a garin Kismayo dake kudancin Somaliya, inda sojojin gwamnatin kasar suka fatattaki mayakan, kafin daga bisani kuma suka dauki matakan sojan hadaka tare da sojojin Amurka dake Somaliya don kashe mayakan al-Shabab guda 73, tare da lalata wasu motocin kungiyar da dama.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China