Mohamed al-Barghuthi, shugaban tawagar wakilai masu shiga tsakani, shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai bayan sanya hannu kan yarjejeniyar tsakaita bude wutar, "an kuma amince da bude wasu hanyoyi da aka riga aka rufe kuma an bude shingen dake hana al'umma sukuni, da musayar fursunoni da wadanda ake tsare da su, don tabbatar da aiwatar da yarjejeniyar, da kawo karshen kariyar da al'umma da sojoji ke baiwa bata gari."
Wakilin musamman na MDD a Libya Ghassan Salame, ya yabawa yunkurin da masu shiga tsakanin suka yi, inda ya yi fatan samun cikakkiyar aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma matsaya kanta," ofishin wanzar da zaman lafiya na MDD a Libya shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa.
Kudancin Tripoli ya jima yana fuskantar tashe-tashen hankula musamman a cikin 'yan kwanakin da suka gabata tsakanin dakarun dake biyayya ga gwamnati da kungiyoyin masu dauke da makamai da ake kira da suna Seventh Brigade. (Ahmad Fagam)