in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An cafke wani jagoran kungiyar IS a Libya
2019-02-02 16:39:38 cri
Dakarun tsaron Libya, sun cafke wani babban shugaban kungiyar IS a birnin Sirte na kasar a ranar Alhamis.

Wani jami'in ma'aikatar tsaron kasar da ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, dakarun tsaro na musamman ne suka cafke Khalifa Barq a gidansa.

Jami'in ya ce an gudanar da aikin ne bisa bayanan sirri da aka samu game da kasancewar Khalifa Barq a yankin tsakiyar birnin Sirte, inda nan take jami'an tsaro suka dauki mataki, la'akari da kasancewarsa mutum mai hadari, kana daya daga cikin wadanda suka assasa kungiyar IS da Atoney Janar na kasar ke nema ruwa a jallo.

Sirte wanda ke da nisan kilomita 450 daga gabashin Tripoli, ya shafe watannin yana fuskantar gumurzu tsakanin sojojin gwamnatin da MDD ke marawa baya da mayakan IS, wanda ya kawo karshe a watan Disamban 2016, bayan dakarun gwamnati sun karbe iko da garin.

Duk da nasarar da gwamnatin ta samu a Sirte, ta ce har yanzu kungiyar IS barazana ce ga tsaron kasar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China