Jami'ar ta MDD ta bayyana hakan ne a lokacin ganawa da Laila Al-Lafi, babbar jami'ar sashen kula da shirin raya cigaban mata da tallafa musu na gwamnatin Libya.
"Rawar da matan Libya ke takawa wajen gina zaman lafiya da raya cigaba yana da girman gaske," Valle Ribeiro ce ta bayyana hakan.
An kafa cibiyar tallafawa mata karkashin doka mai lamba ta 11 wanda aka amince da ita karkashin yarjejeniyar MDD a kasar Libya, wanda bangarorin 'yan adawa a Libyan suka rattaba hannu kan yarjejeniyar a karshen shekarar 2015, da nufin kawo karshen dambarwar siyasar kasar. (Ahmad Fagam)