in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNSMIL ta yi tir da barkewar fada a kudancin birnin Tripoli
2019-01-17 10:31:18 cri
Tawagar MDD mai aikin wanzar da zaman lafiya a kasar Libya ko UNSMIL a takaice, ta yi Allah wadai da barkewar sabon tashin hankali a kudancin birnin Tripoli fadar mulkin kasar Libiya.

Rahotanni na cewa, fada ya barke tsakanin sojojin gwamnati da wasu mahara masu dauke da makamai. UNSMIL ta ce tana ci gaba da sanya ido kan halin da ake ciki a Libya, tana kuma jan kunnen sassan da ba sa ga maciji da juna, da su kauracewa keta hurumin yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma a watan Satumbar bara.

Rundunar ta ce kazantar tashe-tashen hankula na iya gurgunta yanayin sauyi da aka samu a kasar, zai kuma jefa rayukan fararen hula cikin mawuyacin hali. Kaza lika rundunar ta MDD ta sha alwashin daukar matakan dakile wannan barazana.

Gabanin hakan dai rundunar tsaron birnin Tripoli, dake karkashin ikon ma'aikatar cikin gida, ta tabbatar da aukuwar dauki ba dadi tsakanin sojojin kasar da wasu mahara a kudancin Tripoli. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China