in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya taya al'ummomin Sin murnar sabuwar shekara
2019-02-03 19:45:16 cri
Yau Lahadi, kwamitin tsakiyar Jam'iyyar Kwaminis ta Kasar Sin da majalisar gudanarwar kasar ta Sin sun shirya liyafar taya murnar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar Sin, wanda za a fara a Talata mai zuwa. A madadin kwamitin tsakiyar JKS da majalisar gudanarwar kasar Sin, babban sakataren kwamitin tsakiyar JKS, shugaban kasa, kana shugaban kwamitin soja na tsakiya Xi Jinping, ya taya daukacin jama'ar kasar Sin dake cikin gida da wajen kasar murnar bikin sabuwar shekara.

Xi Jinping ya ce, an sami ci gaban Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da na gwamnatin kasar, sabo da kokarin da al'ummomin kasar suka yi. Tabbas ne, za mu ci gaba da warware dukkanin matsalolin dake gabanmu da kuma cimma nasarori, idan mun ci gaba da dogaro kan al'ummomin kasar. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China