in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bikin Bazara: An fara jigilar mutane zuwa yankunansu
2019-01-21 11:20:11 cri

Yayin da bikin bazara na shekara ta 2019 ke karatowa, wato biki mafi kasaita ga al'ummar Sinawa, daga yau Litinin ne, aka fara jigilar mutane zuwa yankunansu. A halin yanzu, ana dada inganta hanyoyin sufuri daban-daban a kasar Sin kuma ana kara saukaka zirga-zirga ga jama'a.

Tun bayan da gwamnatin kasar Sin ta fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, ake kara samun mutanen dake barun yankunan su suna zuwa yin aiki ko karatu a manyan birane da garuruwa, al'amarin da ya sa a lokacin bikin bazara, suke komawa yankunansu don haduwa da iyali, kana kuma za su koma wuraren ayyukansu bayan bikin. Daga shekara ta 2012 ya zuwa yanzu, a kowace shekara akan yi jigilar mutanen a yayin bikin bazara a kasar Sin da yawansu ya kai kimanin biliyan uku.

A matsayin wata muhimmiyar hanyar jigilar fasinjoji, jigilar fasinjoji ta layin dogo a kasar Sin zai karu da kashi 5 bisa dari a yayin bikin bazara, yayin da jigilar fasinjoji ta jiragen kasa masu gudun gaske zai karu da kashi 17 bisa dari.

Har wa yau, hukumomin kula da jiragen kasa da na sama na kasar Sin suna daukar wasu sabbin matakai don kara saukaka tafiye-tafiye ga fasinjoji.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China