in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi bikin taya murnar sabuwar shekara ta Sin a Nijeriya
2019-02-03 16:11:53 cri

Jiya Asabar, an yi bikin baje-kolin al'adun sinawa mai taken "Murnar Bikin Bazara" na shekarar 2019 a cibiyar al'adun kasar Sin dake birnin Abuja, fadar mulkin Nijeriya.

An yi wannan biki cikin hadin gwiwar ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Nijeriya da cibiyar al'adun Sin ta kasar Nijeriya, ban da haka kuma, kungiyar kasuwancin kasar Sin dake kasar Nijeriya ta bada taimako wajen gudanarwar bikin.

Zaunanniyar sakatariyar ma'aikatar harkokin labarai da al'adu ta kasar Nijeriya Grace Isu Gekpe ta bayyana cewa, an shirya bikin baje-koli al'adun sinawar ne domin taya murnar zagayowar bikin bazara da na sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin a kasar Nijeriya, kuma wannan ya kasance kyakkyawar musayar al'adu dake tsakanin Sin da Najeriya. Ta kuma kara da cewa, muna yin musayar al'adu a tsakanin kasashen Sin da Nijeriya, domin habaka kayayyakin al'adunmu zuwa kasashen duniya. Mutanen da suka ziyarci wannan biki, ba Sinawa ba ne kadai, har ma da mutanen Nijeriya da dama da ma wasu mutanen kasashen waje. Mahalarta bikin dai, za su samu damar kara ilminsa game da bikin baje-kolin al'adun kasar Sin, lamarin da zai tallafawa dukkan al'ummomin duniya baki daya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China