Sama da bukukuwa 1,500 ake saran gudanarwa, da nune nunen al'adun gargajiyar Sinawa, wannan na daga cikin shirye shiryen da za'a gudanar a wannan shekara, wadanda ake saran za'a gudanar da su a birane 396 dake cikin kasashe da yankunan duniya 133 a lokacin wannan shagali.
Shirin na "murnar sabuwar shekarar Sinawa" na kasa da kasa, ya kunshi batutuwan raya al'adun gargajiya da bikin bazara a duk fadin duniya, a shekarar 2010 aka kaddamar da wannan shiri na yin musayar al'adu tsakanin kasar Sin da sauran kasashen duniya a karon farko.