Kasar Sin tana sa ran samun karuwar adadin tafiye tafiye a lokacin bikin bazara dake tafe, Lian Weiliang, mataimakin shugaban hukumar raya cigaban da sauye-sauye na kasar Sin ne ya bayyana hakan, a yau Jumma'a.
A tsawon lokacin tafiye tafiyen da za'a gudanar tsakanin ranar 21 ga watan Janairu zuwa 1 ga watan Maris, ana sa ran masu tafiye-tafiyen za su yi bulaguro da yawansa ya kai biliyan 2.99, wanda ya karu da kashi da 0.6 a makamancin lokacin bara, Lian ya bayyana hakan ne a taron manema labaru.
Miliyoyin Sinawa ne ke komawa zuwa garuruwansu na asali a duk shekara a lokain hutun sabuwar shekara domin ganawa da iyalansu. Shekarar 2019, shekara ce ta alade bisa ga kalandar gargajiya wanda za ta fara daga ranar 5 ga watan Fabrairu.(Ahmad Fagam)