An gama aikin shirya bikin kade-kade da raye-raye na murnar shiga sabuwar shekara
Da daren jiya Asabar ne, wakilin ofishin siyasar kwamitin tsakiyar JKS, kana shugaban hukumar kula da harkokin fadakar da jama'a na kwamitin tsakiyar JKS Huang Kunming, ya kai ziyara a dandalin gwajin bikin kade-kade da raye-raye na murnar shiga sabuwar shekara, dake babban gidan rediyo da telabijin na kasar Sin CMG, inda ya nuna kyakkyawan fata ga masu wasan kwaikwayo, da ma'aikatan CMG, domin zuwan bikin bazarar kasar Sin. Ya kuma sa kaimi ga masu wasan kwaikwayo da su shirya bikin cikin himma da kwazo, ta yadda za a nuna nagartaccen fatan alheri ga al'ummomin kasar Sin dake cikin gida da na waje.
Bayan shiryawa da gwaje-gwajen da aka yi sau da dama, ya zuwa yanzu, an gama aikin shirya bikin kade-kade da raye-raye na murnar shiga sabuwar shekara da za a gabatar a ranar 4 ga watan Fabrairu, wato jajiberin bikin sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin ta talabijin. Haka kuma, bisa babban taken bikin, wato "Za mu dukufa don shiga sabon zamani, za mu kuma ji dadin sabuwar shekara", shirye-shiryen kade-kade da raye-raye na bikin, za su nuna sabon ci gaba da aka samu wajen raya zamantakewar al'umma, da kuma sabbin sakamakon da aka samu game da yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje. (Maryam)