Jiya Litinin, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya kira zaunannen taron majalisar gudanarwar kasar Sin, inda ya yi kira da a kara bada goyon baya ga kamfanoni masu zaman kansu, da kuma kanannan da matsakaitan kamfanoni. Haka kuma, an yanke shawarar soke iznin bude ajiyar banki, da kuma rage lokacin gudanar da bincike kan lambar kira da tambarin ciniki.
A yayin taron, an ce, kara taimakawa kamfanoni masu zaman kansu, da kuma kanana da matsakaitan kamfanoni bisa kudurin kwamitin tsakiyar kasar Sin, zai ba da gudummawa ga bunkasuwar tattalin arziki na cikin gida, da samar da sabbin fasahohi, da kuma samar da karin guraben aikin yi a kasar. (Maryam)