in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin ya yi kira da a kirkiro fasahohin da za su taimakawa samun ci gaba
2018-12-07 10:47:10 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqian, ya yi kira da a zurfafa sauye-sauye domin bada kwarin gwiwar kirkire-kirkire a cikin al'umma, tare da kirkiro fasahohin da za su taimaka wajen samun ci gaba.

Li Keqiang wanda mamba ne a kwamitin gudanarwar hukumar kula da harkokin siyasa ta JKS, ya yi wannan kira ne yayin zama na farko na kwamitin kasar, dake jagorar ayyukan kimiyya da fasaha, wanda ya ke shugabanta.

Firaministan wanda ya ce kirkire kirkire na da muhimmanci ga makomar kasar, ya ce a yayin da take gudanar da sauye sauye da daga darajar tsarin tattalin arzikinta, ya kamata Sin ta inganta karfin ta na yawan al'umma da kasuwarta na cikin gida, wajen fadada kirkire kirkire da samar da ci gaba mai inganci.

Ya yi kira da a mayar da hankali kan muhimman fasahohi da za su zama jigon samun ci gaba da inganta hade fasaha da tattalin arziki.

Ya yi kira da a zurfafa sauye-sauye ga tsarin lura da fannin kimiyya da fasaha tare da bada kariya mai karfi ga hakkin mallakar fasaha da kuma samar da kyakkywan yanayin kirkire kirkire. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China