An soma shirye-shiryen murnar bikin bazara na shekarar 2019 a fadin duniya
Yau ne aka shirya taron manema labarai dangane da soma shirye-shiryen bikin bazara na shekarar 2019 a duk fadin duniya a nan birnin Beijing. Rahotanni na cewa, yayin bikin bazara na gargajiyar kasar Sin na bana, ana saran za a gudanar da shagulgula sama da 1500 a kasashe da yankuna 133 na duniya, domin murna da more al'adun Sinawa tare da jama'ar kasashe daban daban. (Bilkisu)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku