in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta jaddada aniyar tallafawa majalisun kananan hukumomin kasar Libya
2019-01-07 09:35:29 cri
Stephanie Williams, mataimakiyar wakilin musamman na babban sakataren MDD game da al'amurran siyasar kasar Libya, ta nanata bukatar tallafawa majalisun kananan hukumomin kasar Libya.

Williams, ta bayyana hakan ne a lokacin ganawa da Milad Taher, ministan kula da kananan hukumomin kasar Libyan, a Tripoli babban birnin kasar, inda jami'an biyu suka tattauna game da yin hadin gwiwa da kuma rawar da kananan hukumomin kasar zasu taka.

A ranar Alhamis, Williams ta gana da Salem Bentahia, shugaban kwamitin tsare tsaren shirya zabukan majalisun kananan hukumomin, kana ta bayyana cikakken goyon MDD game da yin rejistar masu zabe da kuma shirye-shiryen gudanar da zabukan kananan hukumomin wanda za'a gudanar a watan Maris.

Libya tana da majalisun kananan hukumomi sama da 100 wadanda ke wakiltar birane da yankuna daban daban na kasar.

Wa'adin shugancin majalisun kananan hukumomin kasar da aka zaba a shekarar 2014 ya kare. Bisa ga dokokin zaben kananan hukumomin ana bukatar shafe wa'adin shekaru 4 ne ba tare da yin tazarce ba.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China