in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nutsewar jirgin ruwa a Djibouti ya hallaka mutane 52
2019-01-31 19:17:36 cri
Hukumar dake lura da masu kaura ta kasa da kasa IOM, ta ce yawan wadanda suka rasu sakamakon nutsewar wasu kwale-kwale biyu, na bakin haure a kusa da bakin tekun Djibouti ya kai mutane 52.

Wata sanarwa da IOM ta fitar, ta ce ya zuwa ranar Laraba, tawagar masu aikin ceton bakin hauren, ta gano 52 daga wadanda hadarin ya rutsa da su. A ranar Talata an gano wasu maza uku da mata biyu, kana a Laraba aka gano gawawwakin mutane 47.

Sanarwar ta ce akwai kuma mutane 16, da suka tsallake rijiya da baya a Obock, dake bakin tekun na Djibouti. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China