in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakin shugaban kwamitin aikin soja na JKS ya kai ziyara a Djibouti
2016-11-25 10:56:10 cri
Tun daga ranar 23 zuwa 24 ga wannan wata, mataimakin shugaban kwamitin aikin soja na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin wato JKS Fan Changlong, ya kai ziyarar aiki a kasar Djibouti, inda ya gana da shugaban kasar Ismail Omar Guelleh, tare da yin shawarwari tare da firaministan kasar Abdoulkader Kamil Mohamed.

Fan Changlong ya bayyana cewa, a watan Disambar bara, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugaba Guelleh a wajen taron koli na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar Sin da Afirka, inda suka cimma daidaito kan kara yin imani da juna a fannin siyasa, da kara yin hadin gwiwarsu a dukkan fannoni, da yin kokarin samun moriyar juna da bunkasuwa tare a tsakanin kasashe masu tasowa. Kana Sin tana son yin aiki tare da Djibouti wajen aiwatar da ayyukan da shugabannin kasashen biyu suka cimma daidaito kansu, da inganta dangantakar dake tsakaninsu zuwa wani sabon mataki.

A nasa bangare, Guelleh, ya yabawa kasar Sin saboda goyon bayan da take nunuwa kasarsa, da kuma samar da gudummawa ga kasar ta Djibouti, ya ce, kasarsa ta dora muhimmanci sosai kan dangantakar dake tsakanin sojojin kasashen biyu, kana tana fatan za ta ci gaba da yin hadin gwiwa tare da kasar Sin a fannonin siyasa, tattalin arziki, aikin soja da dai sauransu.

Haka zalika, Kamil ya bayyana cewa, Djibouti da Sin suna sada zumunta mai kyau, kasar Djibouti tana son samar da gudummawa ga kasar Sin yayin da take gudanar da wasu ayyuka a nahiyar Afirka, kana tana fatan kasashen biyu za su zama abokai masu kyau dake nuna goyon baya ga juna har abada. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China