Manufar bude wannan sansanin dai, ita ce baiwa kasar Sin damar sauke nauyin dake kanta a harkokin kasa da kasa, musamman ba da agajin jin kai da kuma yiwa jiragen ruwa dake zirga-zirga a yankin ruwayen Somaliya da tekun Aden rakiya.
A ranar 11 ga watan Yulin wannan shekara ce aka kafa sansanin sojojin PLA a kasar Djibouti, bisa shawarar kasashen Sin da Djibouti, zai kuma taimakawa kasar Sin cika alkawuranta kan harkokin kasa da kasa.
An gudanar da fareti tare da kafa tutar kasar Sin yayin wannan biki da ya gudana a barikokin sansanin sojojin na PLA. (Ibrahim Yaya)